Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Takardun da aka fallasa sun nuna cewa an yi jigilar hotunan ne a cikin watannin farko na fara kisan kare dangi a Gaza, kuma wani sashe na soji da aka fi sani da "Rolling Stone" wanda ke da babban rumbun bayanai da ke ɗauke da hotuna da bayanai kan Falasɗinawa ne ya aiwatar da shi.
Takardun suna nuni da cewa sashen "Rolling Stone" yana daga cikin muhimman abokan cinikin sojin Isra'ila a wurin AWS. Waɗannan takardun wani ɓangare ne na bincike kan dogaron sojin Isra'ila kan fasaha da tsarin ayyukan lissafin girgije na kamfanin Amazon wajin "sa ido kan Falasɗinawa".
Dangane da fayilolin da kuma tattaunawa da majiyoyin soji da The Guardian ta ruwaito, Isra'ila cikin shekarun da suka gabata ta kai ɗimbin bayanai — ciki har da kayan leƙen asiri masu muhimmanci da bayanai kan Falasɗinawan da ke zaune ƙarƙashin mamayewa — zuwa cibiyoyin bayanai na Amazon. An kai tarin hotunan zuwa wata cibiyar bayanai ta kamfanin kusa da Tel Aviv ta hanyar wani sashe da aka fi sani da "Rolling Stone" wanda ke cikin wata rundunar software ta soji.
Takardun, a cewar The Guardian, suna fallasa zurfin haɗin gwiwa tsakanin sojin Isra'ila da kamfanin Amazon, a cikin tsarin kwangilar "Project Nimbus" da aka sanya hannu a shekarar 2021, wanda ke ba gwamnati da cibiyoyin sojin Isra'ila damar amfana daga ayyukan lissafin girgije da ajiya da sarrafa bayanai. A ƙarƙashin wannan shiri, AWS ta buɗe sabbin cibiyoyin bayanai a Isra'ila a farkon shekarar 2023, abin da ya ba gwamnatin Isra'ila da abokan cinikinta na soji damar canja da bayanai daga sabar su ta sirri, dake dauke da takardun.
Fayilolin suna nuni da cewa ɗaya daga cikin manyan sassan shirin shine alkawarin AWS na ba wa sojin damar shiga wani yanki keɓantacce cikin cibiyoyin bayananta a Tel Aviv, wanda aka kiyaye shi da matakan tsaro na dijital da na zahiri ingantattu.
A farkon shekarar 2024, wata ƙaramar ƙungiyar sojojin Isra'ila ta yi aiki daga ofisoshin kamfanin AWS a Tel Aviv, kuma majiyoyin soji da yawa sun ambata cewa sojojin suna neman hanyoyin amfani da ababen more rayuwar girgijen kamfanin wajin gudanar da shirin gane fuska da ake aiwatarwa a Gaza cikin inganci mai yawa, a cewar jaridar.
Dangane da haka, takardun suna haskaka amfani da sojin ababen more rayuwar AWS wajin tallafawa tattarawa da sarrafa bayanan sirri na Falasɗinawa, waɗanda yawanci ake tattara su ba bisa ka'ida ba, ta hanyoyin shiga tsakani kuma ba tare da yardarsu ba.
The Guardian a shekarar da ta gabata ta fallasa cewa shirin yana ɗauke da sharuɗɗa marasa dadi da ke hana kamfanonin Amurka iyakancewa ko dakatar da amfani da gwamnati da sojin Isra'ila na ayyukan lissafin girgijen su, ko da Isra'ila ta keta sharuɗɗan sabis ɗinta.
A cewar jaridar, dogaron sojin Isra'ila kan ayyukan AWS yana nuni da karɓuwarsa — cikin shekarun da suka gabata — ga manyan kamfanonin fasaha na Amurka wajen biyan buƙatun fasaha na yaƙi ta hanyar ajiya mai saurin faɗaɗawa, ƙarfin lissafi da ayyukan da basirar wucin gadi ke tallafawa.
Fayilolin suna nuna cewa ma'aikatar ta mayar da ɗimbin bayanan da take riƙe da su zuwa abin da ake kira "gonar katanga" cikin girgijen AWS cikin shekarar 2023 gaba ɗaya. A baya jaridar "New York Times" ta wallafa wani rahoto kan yadda sojin ya gwada fasahar da ake samu a kasuwa a Gaza wajin gano fuskoki cikin taron jama'a da hotunan jiragen mara matuƙa.
Isra'ila ta sha amfani da fasahar "gane fuska", musamman a mamayar da take yi wa Yammacin Kogin Jordan, inda ake ɗaukar hoton fuska a matsayin mataki na yau da kullum a "mashigai", a lokacin da sojojin Isra'ila ke amfani da manhajojin wayoyin hannu da aka ƙera musamman wajin tattara hotunan mutanen da ke zaune a yankunan Falasɗinu.
Ya kamata a lura cewa, "mashigai da shingayen soji" tsari ne mai cikakken iko da ke takaita 'yancin motsi kuma ya mayar da rayuwar Falasɗinawa a Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza zuwa killacewa na yau da kullum da ke shafar sassan yanayin ƙasa, tattalin arziki da ɗan adam na rayuwarsu, sakamakon keɓe biranen da ƙauyuka, da rarraba yankuna zuwa ƴan yankuna daban-daban na yanayin ƙasa, abin da ke sa tafiya tsakanin birni da wani ko har tsakanin ƙauye da cibiyar gundumarsa ya zama mai rikitarwa da ke buƙatar dogonnin sa'o'i.
…………………
Ra'ayinka